Rundunar Sojojin Hadin Gwiwa ta Yankin Arewa maso Gabas, wato Operation HADIN KAI (OPHK), ta kashe ’yan ta’adda 16 tare da ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su a jerin farmakin da ta kai a Jihar Borno.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hedikwatar Rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa sojojin sun yi nasarar fatattakar wani hari da mayakan ISWAP suka kai kan sansanin soji na Forward Operating Base (FOB) Auno da misalin ’yan mintuna kaɗan kafin ƙarfe 12 na dare a ranar 5 ga Fabrairu, 2026.
Ya ce sojojin Sashen 1 sun dakile harin cikin kwarewa da tsantsar shiri, lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya.
Haka kuma, a ranar 9 ga Fabrairu, 2026, sojojin tare da hadin gwiwar ’yan Civilian Joint Task Force (CJTF) sun kaddamar da farmakin ramuwar gayya a yankin Komala da ke Karamar Hukumar Konduga.
Rahoton ya ce sojojin sun bi sawun ’yan ta’addan har zuwa yankin Gidan Kaji da ke kan titin Maiduguri–Damboa, inda suka kashe ’yan ta’adda 16, yayin da wasu suka tsere dauke da raunuka.
An kuma kwato fiye da kekuna 20, makamai da sauran kayayyakin da ’yan ta’addan ke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun kama wasu da ake zargi masu samar wa ISWAP kayayyakin tallafi, inda aka cafke su da tarin magunguna da ake zargin an nufa a kai wa ’yan ta’addan a yankin Bukarti.
A wani bangare na daban, sojojin sun dakile wani yunkurin sace mutane a kan titin Buratai–Kamuya–Biu da misalin karfe 5:20 na yammacin ranar 9 ga Fabrairu.
Bayan bin sahun maharan cikin gaggawa, ’yan ta’addan sun watsar da mutanen da suka sace tare da tserewa cikin daji. An ceto Malam Idris Adamu da Malam Muhammadu Safiyanu, inda aka mika su ga iyalansu a Buratai.
Tags
Labarai
_1.webp)