Bayan Kwanaki 46 da biyan naira miliyan 40, har yanzu ’yan bindiga na cigaba da rike da mutane tara a jihar Kwara.
Mutane tara daga garin Adanla da ke Karamar Hukumar Ifelodun a Jihar Kwara har yanzu suna hannun ’yan bindiga, duk da cewa an biya kudin fansa har Naira miliyan 40 domin a sake su.
Wani dan uwa na wasu daga cikin wadanda aka sace ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa an hada kudin ne ta hanyar gudummawar al’ummar gari da wasu masu hannu da shuni, sannan aka mika wa ’yan bindigar. Sai dai har yanzu ba a saki mutanen ba.
Majiyar ta bayyana cewa ’yan bindigar sun kira su suna mai cewa sun ji rahoton da aka yada a kafafen yada labarai game da sace mutanen, kuma suna jiran ko jami’an tsaro za su kai musu farmaki domin ceto su.
Hakazalika, dan uwan ya zargi wasu masu ba da bayanan sirri a cikin al’umma da taimaka wa ’yan bindigar ta hanyar ba su bayanai.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kwara da hukumomin tsaro da su gaggauta daukar mataki domin tabbatar da kubutar da wadanda ake tsare da su.
An sace mutanen ne a ranar 26 ga Disamba, 2025, a fadar sarkin garin, Oba Olarinoye.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun kai farmakin ne domin neman sarkin da matarsa, wadanda a lokacin ba sa cikin garin, suna Igbaja. Da suka rasa su, sai suka kama mutanen tara tare da tafiya da su cikin daji.
Al’ummar yankin na cikin matsanancin fargaba da damuwa, yayin da har yanzu ba a san halin da wadanda aka sace ke ciki ba duk da biyan kudin fansar mai tsoka.
Tags
Labarai
