Harin Jirgin Sama Mara Matuki a Masallaci ya kashe yara uku a Tsakiyar Sudan.


Harin Jirgin Sama Mara Matuki a Masallaci ya kashe yara uku a Tsakiyar Sudan.

Wani hari da jirgin sama mara matuki ya kai kan wani masallaci a tsakiyar Sudan ya yi sanadin mutuwar yara uku tare da jikkata wasu 13, a cewar wata ƙungiyar likitocin Sudan, yayin da hare-hare makamantan haka ke ƙaruwa a yankin.

Cibiyar Sudan Doctors Network ta bayyana cewa harin ya faru ne da asubahin ranar Laraba, inda ta zargi rundunar Rapid Support Forces (RSF) – wata rundunar soji ta sa-kai da ke gwabza yaÆ™in basasa na tsawon shekaru uku da Rundunar Sojin Sudan (SAF) – da kai harin.

Rahotanni sun nuna cewa yaran na cikin karatun AlÆ™ur’ani ne a Masallacin Sheikh Ahmed al-Badawi da ke Jihar North Kordofan lokacin da jirgin mara matuki ya kai hari kan ginin. Ƙungiyar likitocin ta bayyana harin a matsayin “babban take dokokin jin Æ™ai na Æ™asa da Æ™asa da kuma mummunan hari kan wuraren ibada,” a wani saÆ™o da ta wallafa a shafinta na Facebook.

“Harar yara a cikin masallatai cikakken laifi ne da ba zai samu wata hujjar da za ta kare shi ba, kuma yana nuna wani sabon mataki mai haÉ—ari na maimaita take haƙƙin fararen hula,” in ji Æ™ungiyar.

Sudan Doctors Network ta kuma ce RSF ta taba kai hare-hare kan wasu wuraren ibada a baya, ciki har da wata coci a Khartoum da kuma wani masallaci a el-Fasher, lamarin da ta ce yana nuna “tsarin da ke nuna rashin mutunta rayuka da wuraren ibada.”

Ƙungiyar ta yi kira ga al’ummar Æ™asa da Æ™asa, Majalisar ÆŠinkin Duniya, da Æ™ungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da na jin Æ™ai da su É—auki matakin gaggawa domin matsa lamba a kawo Æ™arshen hare-haren kan fararen hula, tabbatar da kariyarsu, buÉ—e hanyoyin isar da agajin lafiya da na jin Æ™ai, tare da tattara hujjoji domin gurfanar da masu hannu a laifukan gaban kuliya.

A wani ɓangare kuma, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an samu rahotannin jerin hare-haren jirage marasa matuki kan ababen more rayuwa na fararen hula a jihohin South Kordofan, North Kordofan da West Kordofan.

Katafariyar ma’ajiyar Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) a Kadugli ma ta fuskanci hari da ake zargin rokoki ne a daren Talata, a cewar kakakin Majalisar ÆŠinkin Duniya, Stephane Dujarric, wanda bai bayyana wace Æ™ungiya ce ta kai harin ba.

“Kasancewar dole ne mu riÆ™a maimaitawa kusan kullum cewa bai kamata a kai hari kan fararen hula da ababen more rayuwarsu ba, ciki har da wuraren ibada, makarantu da asibitoci, abin takaici ne matuÆ™a,” in ji Dujarric ga manema labarai.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargadin cewa yaƙin basasar Sudan na ƙara faɗaɗa daga yankin Darfur na yamma zuwa yankin Kordofan.

Ta kuma bayyana cewa sama da fararen hula 90 sun mutu, yayin da 142 suka jikkata sakamakon hare-haren jirage marasa matuki tsakanin ƙarshen watan Janairu zuwa 6 ga Fabrairu. Hare-haren, a cewar Majalisar, duka RSF da Rundunar Sojin Sudan ne suka kai su.

Abubuwan da aka kai wa hari sun haÉ—a da ayarin motocin WFP, kasuwanni, cibiyoyin lafiya da unguwannin zama a yankunan Kordofan na arewa da kudu, in ji Majalisar ÆŠinkin Duniya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form