Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka biyar a ranar Talata sun gabatar da kudirin doka da ke neman kakaba takunkumi, ciki har da hana biza da kulle kadarori, kan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma kungiyoyin Miyetti Allah, Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da Miyetti Allah Kautal Hore, da wasu mutane da kungiyoyi.
‘Yan majalisar sun gabatar da kudirin ne a Majalisar Wakilan Amurka, inda suke bukatar tilasta wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka gabatar da cikakken rahoto kan kokarin da Amurka ke yi domin magance zargin laifukan kisan kiyashi akan Kiristoci da ake zargin suna faruwa a Najeriya.
Kudirin dokar mai taken “Dokar 'Yancin Addinin Najeriya na 2026” ya samu daukar nauyi daga ‘yan majalisa Chris Smith, Riley Moore (marubucin kudirin), Brian Mast, Mario Diaz-Balart, da Bill Huizenga.
Masu daukar nauyin kudirin sun bayyana cewa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, “ya yi abin da ya dace” ta hanyar sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake kallo a matsayin mai nuna fifiko akan wane bangare dangane da batun ‘yancin addini.
A cewarsu, ya kamata Amurka ta yi amfani da dukkan hanyoyin diflomasiyya da taimakon jin kai da tattalin arziki da na tsaro domin matsa lamba ga Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta kawo karshen rashin hukunta masu aikata manyan laifuka da tsananta wa addini, tare da kare al’ummomin Kirista da malaman addini da sauran tsirarun addinai da ake kai wa hari.
Bisa tanadin kudirin dokar, ana sa ran Sakataren Harkokin Wajen Amurka zai tantance ko wasu kungiyoyin ‘yan bindiga na kabilar Fulani a Najeriya sun cancanci a ayyana su a matsayin kungiyoyin ta’addanci na kasashen waje.
Wani bangare na kudirin ya ce:
“Ya kamata Amurka ta bayar da agajin jin kai, tare da hadin gwiwar Gwamnatin Najeriya, ta hannun amintattun kungiyoyin farar hula, ciki har da kungiyoyin addini, musamman a jihohin yankin Middle Belt.
“Ma’aikatar Harkokin Waje da Ma’aikatar Kudi ta Amurka su kakaba takunkuman da aka nufa, ciki har da hana biza da kulle dukiya karkashin dokar "Global Magnitsky Human Rights Accountability Act", kan mutane ko kungiyoyin da ake zargi da aikata munanan take-take na ‘yancin addini, ko kuma su sanar da Majalisa dalilan da suka sa ba a kakaba irin wadannan takunkuman ba.”
Kudirin ya ambaci mutanen da kungiyoyin da ake son a duba yiwuwar kakaba musu takunkumi da suka hada da:
– Kungiyoyin Fulani makiyaya masu dauke da makamai a Najeriya;
– Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Jihar Kano;
– Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN); da
– Miyetti Allah Kautal Hore.
Marubucin kudirin, Riley Moore, ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar tsanantawa ta tsari a Najeriya.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta sha musanta wannan zargi, tana mai jaddada cewa mabiya addinin Musulunci da Kiristanci baki daya na fuskantar matsalar rashin tsaro da tashin hankali, musamman ayyukan ta’addanci, ba tare da nuna bambanci na addini ba.
Tags
Labarai
