Sakataren Majalisar Tsaron Iran, Larijani ya Zargi Isra’ila da Kokarin Hana Tattaunawa da Amurka
Babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani, ya zargi Isra’ila da kokarin dakile tattaunawar da ke gudana tsakanin Iran da Amurka kan shirin nukiliyar Iran, domin haddasa sabon rikici da zai dagula yankin Gabas ta Tsakiya.
A wata hira da ya yi da Al Jazeera Arabic yayin ziyararsa a Doha, Qatar, inda ya gana da manyan jami’ai a ranar Laraba, Larijani — sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Koli ta Iran — ya ce Isra’ila na kirkirar hujjoji domin tarwatsa tattaunawar da Amurka, a daidai lokacin da ake cikin wani mataki mai muhimmanci na shawarwari.
“Mu na tattaunawa ne kai tsaye da Amurka kawai — ba mu shiga wata tattaunawa da Isra’ila ba,” in ji shi.
“Duk da haka, Isra’ila ta tsoma baki cikin wannan tsari da nufin lalatawa da kuma dakile shawarwarin.”
Ya kara da cewa dabarar Isra’ila ita ce “dagula yankin baki daya,” yana mai cewa ajandarta ta wuce abin da take ikirarin damuwa da shi kan Iran, yana mai nuni da harin da ya ce Isra’ila ta kai a Doha a watan Satumba da ya shafi jami’an Hamas.
Ya kuma yi kira ga shugabannin yankin da su kasance cikin shiri, yana mai cewa: “Suna caca ba da Iran kadai ba, har ma da Qatar, Saudiyya da Turkiyya.”
Taron Netanyahu da Trump.
A cewarsa, harin da Isra’ila ta kai kan Iran a watan Yuni ya zo ne a lokacin da Tehran da Washington ke tsaka da tattaunawa, lamarin da ya dakatar da shawarwarin bayan an gudanar da zagaye da dama.
A ranar Juma’a, Iran da Amurka sun gudanar da wata tattaunawa ta kaikaice a Muscat, babban birnin Oman, domin neman warware sabanin da ke akwai kan shirin nukiliyar Iran.
Wannan na zuwa ne yayin da Amurka ke kara jibge dakarunta a yankin, tare da barazanar Shugaba Donald Trump na kai hari kan Iran idan ba ta amince da bukatunsa ba.
Yayin da ake tattaunawa kan shirya zagaye na gaba, Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kai ziyara Washington domin ganawa ta gaggawa da Trump, inda ya gabatar masa da “ka’idoji” kan yadda ya kamata a tafiyar da tattaunawar da Iran.
Bayan ganawar, Trump ya ce “ba a cimma wata yarjejeniya ta karshe ba,” sai dai ya jaddada cewa ya nace kan ci gaba da tattaunawa domin duba yiwuwar cimma yarjejeniya.
Matsaya kan Makamai da Inganta makamashin Uranium.
Larijani ya bayyana cewa har yanzu Tehran ba ta karbi wata takamaiman shawara daga Amurka ba, kuma tattaunawar da aka yi a Muscat ta takaitu ne ga musayar sakonni.
Ya ce akwai fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu cewa Iran ba ta da niyyar mallakar makamin nukiliya — batu da Iran ke yawan jaddadawa.
Sai dai ya nanata cewa tattaunawar za ta takaita ne kan shirin nukiliya kadai, ba za a taba batun shirin makamai masu linzami na Iran ba, wanda ya bayyana a matsayin lamari na cikin gida da ya shafi tsaron kasa.
“Haka kuma, batun rage inganta uranium zuwa sifili ba ya cikin tattaunawar,” in ji shi, yana mai cewa hakan ba zai yiwu ba ga kasa da ta riga ta mallaki fasahar, musamman ganin ana bukatar uranium mai inganci don ayyukan farar hula kamar jinyar cutar daji.
Ya kuma bayyana cewa Iran a shirye take ta amince da bincike da tabbatarwa kan shirinta na nukiliya.
Barazanar Martani.
Larijani ya gargadi cewa idan Amurka ta sake kai hari kan Iran, kamar yadda ta yi a watan Yuni kan cibiyoyin nukiliya a yakin kwanaki 12 na watan Yuni, Iran za ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan sansanonin sojin Amurka a yankin.
Kafin barin Doha, Larijani ya kuma gana da shugaban Majalisar Jagorancin Hamas, Muhammad Darwish, tare da wata tawaga, domin tattauna halin da ake ciki a yankin da kuma yakin Gaza, kamar yadda kafar Al-Manar ta ruwaito.
Aljazeera
Tags
Labarai
