‘Yan bindiga sun yi barazanar kai hari wani kauye idan ba'a basu naira miliyan 100 ba, a Jihar Kebbi.

‘Yan bindiga sun yi barazanar kai hari wani kauye idan ba'a basu naira miliyan 100 ba, a Jihar Kebbi.

Wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun aika da barazanar kai hari ga al’ummar Utouno dake karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 100, in ba haka ba za su kai musu hari.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan barazana ta iso ne cikin wani wasiƙa da aka tura wa shugabannin al’ummar yankin, inda ‘yan fashin suka yi gargadi cewa za su yi amfani da tashin hankali idan bukatarsu ba ta biya ba.

Shugabannin addini da mazauna garin sun nuna damuwa sosai kan wannan barazana, suna neman tallafin hukumomi don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A cewar gwamnatin jihar Kebbi, an riga an ƙara yawan jami’an tsaro a yankin da aka kai barazanar domin hana aukuwar wani mummunan lamari.

Masu lura da tsaro sun ce wannan lamari na nuna yadda har yanzu ‘yan fashi da makami ke zama babban kalubale a wasu sassan Arewacin Najeriya, musamman ma a jihar Kebbi da makwabtanta, inda ake kai hare-hare da satar shanu da satar mutane don kudin fansa.

News Translation in English Language.

Bandits Threaten Kebbi Community, Demand ₦100 Million or Face Attack.

Kebbi, Nigeria: Suspected armed bandits have issued a threat to residents of a community in Kebbi State, demanding the payment of ₦100 million or risk a violent attack.

According to reports, the threat targets Utouno community in Ngaski Local Government Area. The message was reportedly delivered through a letter addressed to community leaders, warning of dire consequences if the demand is not met.

The development has sparked fear and anxiety among residents, with community and religious leaders calling for urgent intervention to protect lives and property.

In response, the Kebbi State Government said it is aware of the threat and has begun implementing enhanced security measures, including the deployment of additional security personnel to the affected area.

Security analysts note that the incident highlights the persistent challenge of banditry in parts of northwestern Nigeria, where communities continue to face threats of extortion, kidnappings, and violent attacks.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form