Rikici mai tsanani ya ɓarke a wasu sassan ƙasar Mexico bayan jami’an tsaron ƙasar sun kashe Nemesio Rubén Oseguera Cervantes, wanda aka fi sani da El Mencho, shugaban ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi ta Jalisco New Generation Cartel (CJNG) — ɗaya daga cikin mafi hatsari da ƙarfi a ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe El Mencho ne yayin wani gagarumin farmakin soji a jihar Jalisco, lamarin da ya haddasa hare-haren ramuwar gayya daga mambobin cartel a jihohi da dama.
An kona motoci, an toshe manyan tituna, kuma an kai hare-hare kan ofisoshin gwamnati da cibiyoyin kasuwanci, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba.
A wasu wurare, an bayar da umarnin mutane su zauna a gidajensu, yayin da aka ƙara yawan jami’an tsaro domin daƙile rikicin. Hukumomi sun tabbatar da asarar rayuka da jikkatawa, ciki har da jami’an tsaro, yayin da zirga-zirgar jiragen sama da harkokin kasuwanci suka fuskanci tsaiko.
Gwamnatin Mexico ta bayyana cewa kashe El Mencho babban nasara ce a yaƙin da take yi da ƙungiyoyi masu aikata laifuka, tana mai jaddada aniyarta na ci gaba da murƙushe duk wata barazana ga tsaro da zaman lafiyar ƙasa.
Sai dai masana tsaro sun yi gargadin cewa gibin shugabanci a cikin cartels na iya haifar da ƙarin tashin hankali yayin da ƙungiyoyi ke fafatawa don karɓar iko.
Hukumomi sun shawarci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan yayin da ake ci gaba da aikin tabbatar da tsaro a yankunan da abin ya shafa.
Tags
Labarai
