Akalla matafiya shida sun fada hannun ’yan bindiga a kan hanyar Naka zuwa Makurdi da ke Benue, a safiyar Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne kusa da wani kauye a hanyar, inda ’yan bindigar suka tare motar matafiyan tare da tilasta musu bin su zuwa daji. An ce mutum guda ya tsere, yayin da aka sace maza uku da mata uku.
Majiyoyi sun ce matafiyan suna tafiya ne cikin tawaga, bayan sun kwana a Ankpa, Jihar Kogi, sakamakon fargabar tsaro a hanya. Bayan sace su, ’yan bindigar sun nemi kudin fansa har Naira miliyan 100 domin sakin wadanda aka kama.
Jami’an tsaro a Makurdi sun ce suna kokarin gano maboyar ’yan bindigar tare da hada kai da al’umma domin ceto wadanda aka sace. Haka kuma, an shawarci matafiya da su yi taka-tsantsan yayin amfani da manyan hanyoyi a yankin.
