Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kashe wasu ‘yan bindiga sannan ta kama mutane 17 a wani gagarumin farmakin tsaro da aka gudanar a wasu sassan jihar.
Wannan farmakin ya gudana ne daga ranar 10 zuwa 13 ga watan Fabrairu, 2026, inda jami’an tsaro suka bankado sansanonin ‘yan bindiga tare da kwace manyan makamai da miyagun kwayoyi.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce an gudanar da ayyukan ne domin murkushe ayyukan ‘yan bindiga a yankunan Kajuru da Tafa da Igabi da Kauru.
A yayin musayar wuta, wasu daga cikin ‘yan bindigar sun mutu, yayin da jami’an tsaro suka samu nasarar kama mutane 17 da ake zargi da taimakawa masu laifin.
An tabbatar da cewa wadanda aka kama suna samun kulawar lafiya, yayin da rundunar ta ce zata ci gaba da irin wannan aiki tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar, ya yin da suke rokon al’umma su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro don tallafawa ayyukan tsaro.
Tags
Labarai
