Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari gidan Babban Liman na Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Ibrahim Sani, inda suka sace matansa da ‘ya’yansa da wasu ‘yan uwansa a jihar Bauchi.
Rahotanni daga garin Dagalai, karamar hukumar Gwana, Alkaleri, sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daren Asabar, 14 ga watan Fabrairu, 2026.
Wani masani kan harkokin tsaro, Malam Musa Bakatsine, ya bayyana cewa majiyoyi daga cikin garin sun tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun yi awon gaba da mutane da dama daga gidan limamin a cikin dare.
“Muna samun labarin cewa a daren jiya, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari a gidan Sheikh Ibrahim Sani, inda suka sace matansa da ‘ya’yansa da wasu ‘yan uwa.
An ce an yi amfani da duhun dare ne wajen kwashe wadanda suka yi niyya zuwa wani wuri da ba a sani ba,” in ji Malam Bakatsine.
An ce wannan mummunan lamari ya jawo tsoro da fargaba a cikin al’ummar Musulmi na yankin, yayin da ke kara bayyana matsanancin halin rashin tsaro da ke addabar wasu sassa na kasar.
Tags
Labarai
