Gwamnatin Sokoto ta ware naira biliyan 1 don ciyar da jama’a a watan Ramadan, inda za'a raba abinci 34,000 a kullum.

Gwamnatin Sokoto ta ware naira biliyan 1 don ciyar da jama’a a watan Ramadan, inda za'a raba abinci 34,000 a kullum.

Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da ware Naira biliyan ɗaya (₦1bn) domin aiwatar da shirin ciyar da jama’a a watan Ramadan na bana, inda ake sa ran raba abinci kimanin 34,000 a kullum ga marasa galihu da sauran mabukata a faɗin jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu ne ya ƙaddamar da shirin, yana mai bayyana cewa manufarsa ita ce rage wa al’umma raɗaɗin rayuwa a lokacin azumi tare da ƙarfafa zumunci da tausayi da taimakon juna a tsakanin jama’a.

A cewar gwamnan, an ƙara yawan cibiyoyin ciyarwa daga 155 zuwa 170 cibiyoyi, inda kowace cibiya za ta rika ba da abinci ga kusan mutane 200 a lokaci guda. 
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tabbatar da tsafta da inganci da dacewar abincin da ake rabawa, tare da ɗaukar ƙarin ma’aikata domin tabbatar da ingantaccen gudanar da shirin.

Gwamna Aliyu ya bayyana cewa shirin ciyarwar Ramadan na daga cikin manyan tsare-tsaren jin ƙai na gwamnatinsa, tare da wasu ayyuka kamar gyaran masallatai da makarantu, da kuma tallafin kuɗi ga masallatan Juma’a a jihar.

Ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin addini da ’yan kasuwa da masu hannu da shuni da su mara wa shirin baya, domin tabbatar da cewa babu wanda zai kwana da yunwa a wannan wata mai alfarma.

Rahotanni sun nuna cewa shirin ciyarwa da azumi a Sokoto ya shafe kusan shekaru 19 ana aiwatar da shi, inda yake ci gaba da taimaka wa dubban al’umma tare da nuna jajircewar gwamnati wajen rage talauci da bunƙasa walwalar jama’a.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form