Iran ta soki ƙasashen Turai game da ko in kula a tattaunawar nukiliyar ƙasar da Amurka.

Iran ta soki ƙasashen Turai game da ko in kula a tattaunawar nukiliyar ƙasar da Amurka.

Ministan harkokin wajen Iran, Seyed Abbas Araghchi, ya yi kakkausar suka ga ƙasashen Turai, yana zarginsu da rashin tasiri a tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyar Iran da Amurka.

Araghchi ya bayyana cewa ƙasashen Turai uku – Faransa da Birtaniya da Jamus (E3) – sun rasa muhimmanci a wannan batu, yana mai cewa ba su nuna cikakkiyar rawar shiga tsakani ba wajen cimma matsaya. 
A cewarsa, Turai ta kasa yin tasiri mai ma’ana duk da ikirarin da take yi na kasancewa muhimmin ɓangare a harkar diplomasiyya.

Ministan ya kuma yi tsokaci kan taron tsaro na birnin Munich, inda ya ce taron ya zama tamkar “wasa na barkwanci” dangane da batun Iran, yana mai nuna rashin gamsuwa da yadda ake tattauna shirin nukiliyar ƙasarsa a irin waɗannan taruka.

A rahoton da Al Jazeera ta wallafa, Araghchi ya jaddada cewa ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya, musamman na yankin Gulf, sun fi Turai tasiri wajen sauƙaƙa tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a halin yanzu.

Wannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin ci gaba da wata sabuwar tattaunawa tsakanin wakilan Iran da Amurka a birnin Geneva, inda ake sa ran tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi rage takaddama kan shirin nukiliyar Iran da kuma takunkuman da aka kakaba mata.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan matsayar Tehran na iya ƙara rage rawar Turai a tattaunawar nukiliyar, tare da sauya akalar diplomasiyya zuwa ƙasashen yankin da ke da kusanci kai tsaye da rikicin.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form