Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Prof. Nentawe Yilwatda, ya kai ziyara kasuwar singer ta Kano da gobara ta lalata, inda ya nuna juyayi da tausayawa ga ’yan kasuwar da abin ya shafa.
A yayin ziyarar, Yilwatda, ya duba irin asarar da gobarar ta jawo, ciki har da konewar shaguna da dukiyoyin ’yan kasuwa.
Ya bayyana alhininsa kan abin da ya faru, yana mai cewa lamarin ya shafi rayuwar dubban iyalai da ke dogaro da kasuwancin wajen neman abinci da ciyar da iyalansu.
Shugaban na APC ya jaddada cewa jam’iyyar da kuma shugabannin gwamnati ba za su yi watsi da ’yan kasuwar ba.
Ya yi alkawarin tuntuɓar hukumomin da suka dace domin a nemo hanyoyin tallafi da kuma taimakon gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, tare da ɗaukar matakan kariya don hana sake faruwar irin wannan gobara a nan gaba.
’Yan kasuwar sun nuna godiya ga ziyarar da nuna damuwar da shugabannin jam’iyya suka yi, suna fatan samun tallafi na gaggawa da zai taimaka musu su farfaɗo da kasuwancinsu bayan wannan mummunan iftila’i.
Tags
Labarai
