'Yan bindiga sun kashe wani basarake a jihar Ondo a lokacin da suke yunkurin sace shi.

'Yan bindiga sun kashe wani basarake a jihar Ondo a lokacin da suke yunkurin sace shi.

Wasu 'Yan bindiga sun hallaka wani sarkin gargajiya ya yin da suke ƙoƙarin sace shi a daren Laraba, 18 Fabrairu 2026, a ƙauyen Agamo, cikin Ƙaramar Hukumar Akure ta arewa dake Jihar Ondo.

Mamacin, Oba Kehinde Jacob Falodun, sarkin Agamo/Alagamo, ya gamu da ajalinsa ne lokacin da kimanin yan bindiga shida zuwa goma suka shigo fadar sa. 
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa harin ya auku ne a lokacin da sarkin ke ƙoƙarin tsira, amma sai aka harbe shi sannan suka ci gaba da dukan shi da wani abu mai karfi yayin da suke ƙoƙarin ɗauke shi.

Wasu rahotanni sun nuna cewa yan bindigar suna magana da Hausa kuma sun shigo ƙauyen ta hanyar Itaogbolu axis. 
Matar sarkin da iyalansa sun kasance wurin lokacin harin, inda ta bayyana cewa ta gudu tana ganin an kashe mijinta.

Jami’an ‘Yan Sanda na Jihar Ondo sun tabbatar da kisan kuma sun ce sun karɓi rahoton da karfe 7:50 na dare. Rundunar tsaro, ciki har da jami’an Rundunar dabaru ta 'yan sanda da masu farauta da Amotekun, da sauran hukumomin tsaro na gida, suna gudanar da bincike a kusa da wuraren da ake zargin yan bindigar sun buya. 
‘Yan sanda sun yi alkawarin kama masu laifin sannan sun roki jama’a da su bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen kama su.

Kisan sarkin ya ƙara tsoratar da mazauna yankin kan matsalar rashin tsaro da ta addabi sassan Akure ta arewa da sauran Jihar Ondo, inda satar mutane da fashi ke ƙaruwa.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form