An bayar da rahoton cewa wani fashewar iskar gas ya girgiza wata ginin gidaje a birnin Karachi na Pakistan, inda mutane da dama suka mutu bayan wani bangare na ginin ya rushe.
Fashewar ta faru ne da safiyar yau Alhamis, 19 ga Fabrairu 2026, a unguwar Soldier Bazaar No. 3 yayin da iyalai ke shirin cin abincin sahur na farkon watan azumin Ramadan.
Hukumar ‘yan sanda da jami’an ceto sun tabbatar da akalla mutane 16 sun rasa rayukansu, ciki har da mata da yara, yayin da wasu da dama suka ji rauni.
Ayyukan ceto na ci gaba yayin da ake cire tarkacen daga karkashin gine-ginen don neman wadanda har yanzu aka ce suna makale.
Bincike na farko yana nuni da yiwuwar fashewar ta samo asali ne daga yoyon iskar gas, inda mutane a yawancin gidaje ke amfani da bututun LPG saboda ƙarancin iskar gas na yau da kullum.
Shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, ya bayyana Alhininsa kan wannan iftila'i, tare da sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan kuma ya umurci a ba da kulawar lafiya ta musamman ga wadanda suka ji rauni.
Tags
Labarai
