Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 38 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsari da ya faru a Kampani Zurak, cikin ƙaramar hukumar Wase, ta jihar Filato, bayan shakar iska mai guba (carbon monoxide) a ramin hakar ma’adinai da ke karkashin kasa.
Binciken farko ya nuna cewa lamarin ya faru ne sakamakon rashin isasshen shigar iska a ramukan hakar hakar ma'adanan, wanda ya haifar da taruwar iskar mai guba.
Iskar carbon monoxide a turance, wacce ba ta da launi kuma ba ta da wari, ta bazu cikin ramin ba tare da nuna wani alama ba, lamarin da ya sa ma’aikatan suka kasa numfashi, suka suma, daga bisani suka mutu kafin a samu damar ceto su.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kimanin ma’aikata 25 sun tsira da ransu, inda aka gaggauta kai su asibitoci domin samun kulawar gaggawa.
Wasu daga cikinsu na ci gaba da karbar magani sakamakon illar shakar iskar mai guba.
Bayan aukuwar hatsarin, Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe wurin hakar ma’adinan nan take, tare da kafa kwamitin bincike na musamman domin gano ainihin musabbabin lamarin, da tantance ko an bi ka’idojin tsaro da dokokin hakar ma’adinai da suka dace.
Haka kuma, jami’an tsaro sun killace yankin domin hana shiga ba bisa ka’ida ba, yayin da ake gudanar da bincike da daukar samfurori na kimiyya.
Masana sun jaddada cewa wannan lamari ya sake bayyana gibin tsaro da raunin kulawa a wasu wuraren hakar ma’adinai, musamman wadanda ke aiki ba tare da cikakken tsari da kayan kariya ba.
Masu ruwa da tsaki sun yi kira ga hukumomi da kamfanonin hakar ma’adinai da su ƙara tsaurara matakan tsaro da saka kayan kariya na zamani, da horar da ma’aikata, domin kare rayuka da hana sake faruwar irin wannan mummunan hatsari a nan gaba.
Tags
Labarai
