Aƙalla sojojin Najeriya takwas (8) ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 23 suka jikkata bayan da ‘yan ta’adda suka kai hari kan wani sansanin sojoji a Jihar Borno, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.
Majiyoyin sun ce harin ya faru ne a ƙauyen Cross Kauwa, wanda ke kusa da Baga, inda ‘yan bindiga masu tayar da ƙayar baya suka kutsa cikin sansanin sojojin da dare.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun zo ne a kan babura masu yawa, inda suka yi artabu mai tsanani da sojoji kafin su janye.
An bayyana cewa maharan suna da alaƙa da ƙungiyar ISWAP, wadda ta dade tana kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.
A yayin harin, an lalata gine-ginen sansanin, an ƙone motocin sojoji, sannan an kwashe wasu makamai.
Harin na daga cikin jerin hare-haren da ‘yan ta’adda ke ci gaba da kai wa kan rundunar Sojojin Najeriya a sassan jihar Borno, lamarin da ke nuna ƙalubalen tsaro da har yanzu ake fuskanta duk da kokarin da gwamnati ke yi.
Hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike da kuma daukar matakan kariya domin hana sake faruwar irin wannan hari.
Tags
Labarai
_2.webp)