A kalla mutane 12, ciki har da yara 5 ne, suka mutu a wani fashewa da aka samu a wani shagon sayar da kayan wasan wutan murnar sabuwar shekarar 'yan china a birnin Xiangyang na lardin Hubei dake ƙasar ta China, yayin bikin murnar Sabuwar Shekarar ƙasar ta (Lunar New Year).
Hukumar kashe gobara ta kashe wutar wacce ta kama shagon nan da nan bayan fashewar, yayin da aka fara bincike don gano musabbabin faruwan lamarin.
Daga cikin wadanda suka mutu akwai mai shagon da kuma wasu abokan ciniki da suka zo sayen wutar wasan don bikin shekaran.
Fasahar wutar wasan, wacce ake harbawa tana daya daga cikin al’adun Sabuwar Shekarar Lunar a ƙasar China, inda iyalai ke kunna wutar domin kawata lokacin hutu da kawar da sharrin.
Sai dai kuma amfani da wutar wasan yana haddasa mummunan hadari lokaci zuwa lokaci.
Bayan wannan, Ma’aikatar Kula da Gaggawa ta China ta sake fitar da gargadi kan tsaro, tana mai cewa “wutar wasan na daya daga cikin manyan haɗarurruka yayin bikin "shekara" kuma ta bukaci hukumomin yankuna su kara kulawa sosai.
Yawancin birane a baya sun sanya takunkumi ko haramcin amfani da wutar saboda tsaro da ingancin iska, ya yin da wasu hukumomin yankuna suka rage takunkumin inda suke bayar da damar amfani da wuta a karkashin ka’idojin tsaro.
Tags
Labarai
