Iran ta gina ganuwar Siminti mai karfin gaske a wasu wuraren binciken sojojin ƙasar, saboda kauce ma yuwuwar harin Amurka.

Hukumar binciken tauraron dan adam ta nuna cewa Iran ta karfafa wasu muhimman wuraren sojojinta ta hanyar gina babbar ganuwar siminti a sabon gine-gine a cikin wuraren — masu matukar muhimmanci da ake alakanta shi da binciken makaman yaki — sannan suka rufe shi da kasa.

Ana ganin wannan wani mataki ne na nufin kare wurin daga yiwuwar harin sama, yayin da rikicin siyasa tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran ke kara tsananta.

Haka zalika, hotunan tauraron dan adam sun nuna cewa binciken ramukan da ke wasu wuraren nukiliya, ciki har da wadanda aka taba kai musu hari, an rufe ko an karfafa su, yayin da tushen makaman Iran da aka lalata a baya, ake gyarawa.

Wadannan abubuwa sun faru ne a daidai lokacin da tashin hankali a tsakanin kasashen duniya ke karuwa, yayin da tattaunawar diflomasiyya tsakanin Amurka da Iran ke ci gaba, duk da cewa har yanzu tattaunawar na cikin yanayi mai rauni, tare da karuwar sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya a matsayin matakin kiyaye tsaro daga shirin nukiliyar Iran da sauran rikice-rikicen yankin.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form