‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, tare da Kona Motar Shugaban Karamar Hukuma a jihar Kaduna.

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Biyu, tare da Kona Motar Shugaban Karamar Hukuma a jihar Kaduna.

Wasu ‘Yan bindiga da ake zargi sun kai hari a ƙauyen Ugom da ke Kajuru a jihar Kaduna, sun kashe mutane biyu tare da kona motar shugaban karamar hukuma yayin wani taron jana’iza.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne a lokacin da jama’a ke taruwa domin jana’iza, inda ‘yan bindigar suka rika harbe-harbe ba tare da ƙa’ida ba, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici. An bayyana sunayen waɗanda suka rasu a matsayin Bitrus David (mai shekaru 25) da Goma Idi (mai shekaru 40).

A yayin harin, motoci huɗu sun ƙone, ciki har da motar aikin Shugaban Karamar Hukumar Kajuru, Dauda Madaki, da wata mota mallakin wani ɗan siyasa. Shugabannin al’umma sun bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da kira ga gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin Al'umma.

Harin ya ƙara nuna ƙalubalen tsaro da wasu sassan Kaduna ke fuskanta, inda al’umma ke roƙon ƙarin tsaro da hukunci mai tsauri ga masu aikata laifukan.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form