Wani dan bindiga ya kashe mutane 2 a wani filin wasan kankara a ƙasar Amurka.

Wani dan bindiga ya kashe mutane 2 a wani filin wasan kankara a ƙasar Amurka.

Akalla mutane biyu ne su ka rasa rayukansu, yayin da wasu mutum uku suka jikkata, sakamakon wani harbin bindiga da ya auku a yayin wasan kankara na makarantar sakandare a birnin Pawtucket a jihar Rhode Island.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026, yayin da ake tsaka da wasan, inda jama’a da dama ke kallon wasa, har ma ana watsa shi kai tsaye ta yanar gizo. Shaidun gani da ido sun ce harbin ya jefa mutane cikin firgici tare da haddasa rudani a filin wasan.

‘Yan sanda sun ce wanda ake zargi da aikata harbin an same shi ya mutu daga baya, kuma ana kyautata zaton ya kashe kansa ne bayan kai harin. An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa.

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa babu sauran barazana ga jama’a, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano ainihin dalilin da ya haddasa harin, inda aka ce yana iya kasancewa rikicin ƙashin kai ko na iyali.

Rahoton ya janyo Allah-wadai daga al’umma da hukumomi, tare da kara tayar da muhawara kan matsalar yawaitar hare-haren bindiga a Amurka, musamman a wuraren taruwar jama’a da makarantu.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form