Sojojin Amurka 100 sun iso Najeriya domin gudanar da aikin horaswa da bayar da shawarwari ga rundunar Sojin Najeriya.
A cewar jami’an Amurka, sojojin da aka tura ba za su shiga faÉ—a kai tsaye ba, kawai za su mayar da hankali ne kan horaswa da bayar da shawarwari da tallafin fasaha ga rundunar Sojin Najeriya.
Rahoton ya ce wannan mataki ya zo ne bisa roÆ™on gwamnatin Najeriya, domin Æ™ara Æ™arfafa yaÆ™in da Æ™asar ke yi da Æ™ungiyoyin ta’addanci kamar su Boko Haram da ISWAP, musamman a yankunan Arewa maso Gabashin Æ™asar.
Jami’an tsaro sun bayyana cewa aikin zai haÉ—a da:
Horas da sojoji kan dabarun yaÆ™i da ta’addanci
Taimakon leƙen asiri da tsare-tsaren aiki
Inganta amfani da kayan aikin zamani
Gwamnatin Nigeria ta jaddada cewa ikon jagoranci da umarni zai ci gaba da kasancewa a hannun hukumomin tsaron Najeriya, kuma sojojin Amurka za su yi aiki ne bisa yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Masu sharhi na ganin wannan ci gaba na nuna ƙara zurfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya, a wani yunƙuri na dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da ke fama da rikici.
Tags
Labarai
