Gwamnatin Labanon ta ce za a bukaci wata hudu kafin kammala mataki na biyu na shirin karbe Makaman Kungiyar Hezbollah, ya yin da jagororin Hezbollah ke ci gaba da yin turjiya da shirin.
Wannan na zuwa ne bayan kammala mataki na farko na shirin yarjejeniyar zaman lafiya da aka gudanar a baya.
Mataki na biyu na shirin na daga cikin yunkurin da gwamnati ke yi na mayar da makaman Kungiyar Hezbollah karkashin ikon kasar, wanda ya biyo bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta shekaran 2024 da ta kawo karshen rikicin da ya barke tsakanin Hezbollah din da Isra’ila.
Gwamnatin ta bayyana cewa lokacin kammala shirin na iya tsawaita, dangane da karfin sojojin kasar da hare-haren Isra’ila, da yadda al’amura ke gudana a filin aiki.
Sai dai har yanzu, jagororin Hezbollah na bayyana rashin amincewa da wannan yunkuri, suna mai cewa hakan “babban kuskure ne” wanda ke amfani da bukatun Isra’ila, duk da cewa kungiyar na ci gaba da rike manyan makamai a yankin.
Tags
Labarai
