Majalisar Shari’a ta Najeriya ta bayyana cewa ikrarin da Amurka ke yi na cewa ana kisan kiristoci a kasar ba gaskiya bane. Haka zalika, ta kare tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, daga zargin da wasu Amurkawa suka yi masa kan alaka da wannan ikirarin.
Majalisar ta ce rahotannin na Amurka suna rikitarwa kuma ba daidai ba ne, ta kuma bukaci hukumomin Najeriya su dauki matakin da ya dace wajen warware wannan al’amari. Ta jaddada cewa kalubalen tsaro da ake fuskanta a Najeriya ba wani shirin kisan kiristoci bane da aka tsara.
Haka zalika, majalisar dokoki da shugabannin addinai a Najeriya sun yi watsi da wannan zargi, inda suka bayyana cewa lamuran tsaro a kasar suna shafar kowa ba tare da nuna bambanci addini ba.
Masana da kuma malaman addini daga arewacin Najeriya sun tabbatar da cewa, tashe-tashen hankula da ake samu suna da alaka da rashin tsaro da ayyukan ‘yan ta’adda, ba wani shirin kisan kiristoci na gwamnati ba ne.
A makon jiya ne wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi ikirarin cewa wasu dokoki da tashe-tashen hankula a Najeriya na nuna kin addinin kiristanci, inda suka yi kira ga daukan matakan takunkumi kan jami’an da ake zargi.
Sai dai gwamnati da majalisar dokoki a Najeriya sun musanta wadannan ikirari gaba daya.
Tags
Labarai
