Mutane 14 ne su ka mutu Sakamakon jerin wasu Hare-Hare da aka kai a ƙasar Pakistan.

Mutane 14 ne su ka mutu Sakamakon jerin wasu Hare-Hare da aka kai a ƙasar Pakistan.

Akalla mutane 14 ne su ka rasa rayukansu a jerin hare-hare da ‘yan ta’adda suka kai a arewacin Pakistan, ciki har da ‘yan sanda da sojoji 11 da farar hula 3, da yaro daya.

Rahotanni sun ce hare-haren sun faru ne a yau da safe a wasu sassa na jihar Khyber Pakhtunkhwa, inda suka hada da:

Wani harin da aka kai da mota dauke da bama-bamai a cikin makarantar addini a gundumar Bajaur, wanda ya kashe jami’an tsaro da yaro.

Haka zalika Bama-bamai sun tashi a kusa da tashar ‘yan sanda a Bannu, wanda ya hallaka fararen hula biyu sannan wasu suka jikkata.

Sai musayar wuta da aka yi tsakanin ‘yan ta’adda da jami’an tsaro a Shangla, inda aka kashe ‘yan ta’adda 3 da ‘yan sanda 3.

Hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke karfafa ayyukansu a yankunan da ke makwabtaka da Kasar Afghanistan, inda suke kai hare-hare a kan jami’an tsaro da fararen hula.
Ya yin da Jami’an tsaron ke ci gaba da fafutukar murkushe Kungiyar Tehrik‑e‑Taliban Pakistan (TTP) da sauran kungiyoyin masu tayar da kayan baya a yankin.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form