Za'a shiga tattaunawar Nukiliya tsakanin Amurka da Iran zagaye na biyu a birnin Geneva.

Za'a shiga tattaunawar Nukiliya tsakanin Amurka da Iran zagaye na biyu a birnin Geneva.

An shirya muhimmin zagaye na biyu na tattaunawar nukiliya tsakanin Amurka da Iran a ofishin jakadancin Oman da ke Geneva na ƙasar Switzerland.

Tattaunawar ta hada da manyan wakilan Amurka — ciki har da Steve Witkoff da Jared Kushner — da kuma Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi.

Babban batu a tattaunawar shi ne shirin nukiliya na Iran da sassaucin takunkumin tattalin arziki, inda Iran ke neman saukaka takunkumi idan ta rage ayyukan haɓakar makamashi, yayin da Amurka ke neman cikakken biyan bukatun tsaro.

Amurka na neman fadada tattaunawar zuwa wasu batutuwan da ba na nukiliya ba, kamar ajiyar makaman Iran, sai dai Iran ta bayyana cewa zata mai da hankali ne kawai kan takaita shirin nukiliyarta don samun saukin takunkumi, tare da kin amincewa da daina hako uranium gaba daya.

Kwana guda kafin wannan taro, Araghchi ya gana da Daraktan Hukumar Kula da Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, domin gudanar da “zurfin tattaunawar fasaha” tare da masana nukiliya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form