Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan rasuwar mutane 14 da suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Gumbi, da ke ƙaramar hukumar Yauri, lokacin da baki da suka halarci bikin aure ke komawa gida bayan rakiyar amarya zuwa gidan mijinta a ƙaramar hukumar Ngaski. Kwale-kwalen da suke ciki ya kife a tsakiyar ruwa, lamarin da ya jawo asarar rayuka.
An ce kwale-kwalen ya kasance cike da fasinjoji fiye da kima, inda aka bayyana cewa fiye da mutane 100 ne ke ciki a lokacin da hatsarin ya auku. Daga cikin waɗanda suka rasu akwai mata 13 da yaro guda ɗaya.
Gwamna Nasir Idris, wanda ya halarci sallar jana’iza tare da shugabannin gargajiya da al’ummar yankin, ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan da masarautar Yauri da daukacin al’ummar jihar.
Ya buƙaci jama’a su karɓi abin da ya faru a matsayin ƙaddarar Allah, tare da yin addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan, Ya kuma bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.
Gwamnan ya kuma sake jaddada kiran gwamnati ga jama’a kan muhimmancin bin ƙa’idojin tsaro a harkar sufuri ta ruwa, musamman kauce wa ɗora fasinjoji fiye da ƙima, domin hana faruwar irin waɗannan mummunan hatsarori a nan gaba.
Tags
Labarai
