An tabbatar da kashe CSP Muhammad Sani Kabir, DPO na karamar hukumar Rimi a Jihar Katsina, yayin da yake jagorantar wani samame da jami’an tsaro suka kai kan wasu da ake zargin masu satar shanu ne.
Lamarin ya faru ne a garin Magaji, da ke yankin Majen-Gobir, bayan samun bayanan sirri kan motsin wasu ‘yan bindiga a yankin. Samamen hadin gwiwa ne tsakanin jami’an tsaro da wasu ‘yan sa-kai na al’umma.
A yayin artabun da aka yi tsakanin jami’an tsaro da maharan, an samu nasarar hallaka mutum uku daga cikin wadanda ake zargi.
Sai dai kuma, a yayin musayar wuta, bindigar marigayi DPO ta samu tangarda, lamarin da ya bai wa shugaban ‘yan bindigar, wanda aka bayyana sunansa da Maigemu, damar harbinsa har lahira.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro uku sun samu raunuka a yayin artabun, kuma ana kula da su a Asibitin Koyarwa na Katsina.
Haka kuma, an ce wasu mutane biyu da ake zargi da kuma wasu ‘yan mata sun samu raunuka a wasu wurare da ke makwabtaka da inda lamarin ya faru.
An dauki gawar marigayin zuwa Zariya, Jihar Kaduna, domin yi masa jana’iza.
Ma’aikatar Harkokin Tsaro da Cikin Gida ta Jihar Katsina ta bayyana alhininta kan rasuwar jami’in, tare da yabawa jarumtaka da sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnatin jihar ta kuma jaddada kudurinta na ci gaba da yaki da ayyukan ‘yan bindiga a fadin jihar.
Tags
Labarai
