Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ta yanke wa fitacciyar jarumar Kannywood, Saadatu Mohammed Inuwa wadda aka fi sani da Samha, hukuncin daurin watanni shida bisa laifin wulakanta takardar kuÉ—in Najeriya.
AlÆ™alin kotun, Mai Shari’a S.M. Shuaibu, ya yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, 13 ga Fabrairu, 2026, bayan wadda ake tuhuma ta amsa laifinta a gaban kotu tare da neman sassauci.
An gurfanar da ita ne bisa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007, wadda ta haramta lalata ko ɓata takardun kuɗin ƙasa.
Laifin ya samo asali ne daga wani lamari da ya faru a shekarar 2022, inda aka same ta da amfani da takardar kuÉ—i na naira dubu É—aya (₦1,000) wajen goge majina — abin da doka ta ayyana a matsayin wulakantawa da lalata kuÉ—in Æ™asa.
Lauyanta ya roÆ™i kotu da ta yi mata rangwame, yana mai bayyana cewa ta nuna nadama kuma ba ta taÉ“a aikata irin wannan laifi ba a baya. Sai dai kotun ta yanke mata hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, tare da ba ta zaÉ“in biyan tarar naira dubu dari biyu (₦200,000) maimakon zaman gidan yari.
Doka a Najeriya ta tanadi hukunci mai tsauri ga duk wanda aka samu da laifin ɓata ko lalata naira, domin kare daraja da martabar kuɗin ƙasa.
Tags
Labarai
_1.jpeg)