Sojoji Sun Ceto mutum 8 da Aka Sace a lokacin wani bikin Aure a jihar Kano.

Sojoji Sun Ceto mutum 8 da Aka Sace a lokacin wani bikin Aure a jihar Kano.

Sojojin Najeriya daga Brigade ta 3 sun yi nasarar ceto mutane 8 daga cikin 10 da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka sace a yayin wani biki a Dabawa, karamar hukumar Shanono ta Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin masu kai hari sun sanya kayan sojoji ne irin na leken asiri lokacin da suka sace baƙin.

Bayan samun rahoton gaggawa ne, sai dakarun da ke kusa da wurin suka tashi, suka fafata da ‘yan bindigan, sannan suka bi su har zuwa Jihar Katsina a kan titin Gidan Mutum Daya kafin samun tazara daga masu laifi.

An mayar da mutanen da aka ceto ga iyalansu, yayin da ake ci gaba da kokarin gano mutane 2 da suka rage.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form