Yadda ’Yan Bindiga Suka Kashe Mutane 32 a Jihar Niger, tare da Sace wasu da dama.

Yadda ’Yan Bindiga Suka Kashe Mutane 32 a Jihar Niger, tare da Sace wasu da dama.

Aƙalla mutane 32 ne suka rasa rayukansu yayin da ’yan bindiga masu ɗauke da makamai akan babura suka kai wani mummunan hari kan ƙauyuka uku a yankin Borgu na Jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne da tsakar dare, inda ’yan bindigar suka rika harbi kan mazauna ƙauyukan ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama tare da sace wasu mazauna yankin. Inda suka kone Gidaje da wasu gine-gine a yankin.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa ’yan bindigar sun kutsa cikin ƙauyukan ne a lokaci guda, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici. “Sun zo ne da yawa, suna harbi, suna sace mutane, ba mu da inda za mu fake,” in ji shi.

Hukumar ’yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce an tura jami’an tsaro tare da hadin gwiwar sojoji domin tabbatar da tsaro da kuma farautar maharan. 
Haka kuma, an fara kokarin ceto wadanda aka sace.

Wannan harin na zuwa ne yayin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara a sassan Arewacin Najeriya, inda hare-haren ’yan bindiga ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman a yankunan karkara.

Hukumomi sun bukaci al’umma da su bayar da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar kai rahoton duk wani abu da ake zargi, domin dawo da zaman lafiya a yankin.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form