Gwamnatin Kano ta kaddamar da Rabon Shinkafa buhu 54,600 ga marasa karfi a watan Ramadan.

Gwamnatin Kano ta kaddamar da Rabon Shinkafa buhu 54,600 ga marasa karfi a watan Ramadan.

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta fara rarraba shinkafa buhu 54,600 domin tallafawa talakawa da masu ƙaramin ƙarfi a lokacin Ramadan.

An fara raba shinkafar ne a titn Maganda da ke Kano, inda mai magana da yawun gwamna, Sunusi Dawakin-Tofa, ya bayyana hakan.

An shirya motoci 91 cike da buhunan shinkafa don rabawa.

Motoci 44 za su kai kai tsaye ga kananan hukumomi 44 a jihar.

Motoci 47 za a raba su tsakanin wasu mutane da ƙungiyoyi a fadin jihar.

An kafa kwamiti a matakin jihar da kuma kananan hukumomi don tabbatar da cewa rabon ya kasance cikin gaskiya da adalci.

Gwamnan ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da kamfanoni da mutane masu hannu da shuni da su shiga hannu wajen rage nauyin tattalin arziki a kan mazauna jihar Kano.

A halin yanzu, Sanata Barau Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ya yaba da wannan mataki, yana mai cewa zai taimaka wajen rage damuwa a lokacin Ramadan. 
Haka kuma, Shugabar Kungiyar Kananan Hukumomi ta Najeriya (ALGN) reshen Kano ta nuna goyon bayanta, inda ta tabbatar da cewa kananan hukumomi za su tabbatar da adalci a rabon.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form