Sojojin isra’ila sun kashe falasdinawa takwas a hare-haren da suka kai a sassan zirin Gaza.

Sojojin isra’ila sun kashe falasdinawa takwas a hare-haren da suka kai a sassan zirin Gaza.

Rahotanni sun bayyana cewa akalla Falasdinawa takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a sassa daban-daban na zirin Gaza a jiya Asabar.

Majiyoyin kiwon lafiya a yankin sun tabbatar da cewa an samu mace-macen ne a kudancin Gaza, musamman a birnin Khan Younis, yayin da wasu hare-haren suka shafi arewacin yankin ciki har da garin Jabalia.

Lamarin na zuwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka ce an cimma tun watan Oktoban 2025 domin rage tashin hankali a yankin. 

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojin Isra’ila, wato Israel Defense Forces, ba ta fitar da cikakken bayani kan zarge-zargen ba.

Wannan sabon lamari na kara nuna yadda ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da na jin kai a Gaza, inda fararen hula ke cikin mawuyacin hali sakamakon rikicin da ya dade yana gudana a yankin.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form