Yadda Kungiyar 'yan ta'adda masu tsattsauran ra'ayi suka kashe mutune 165 a ƙauyuka biyu na Jihar Kwara.
An samu karin bayani game da adadin wadanda suka mutu a harin da wasu ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra'ayi suka kai kan al’ummar Woro da Nuku na karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara.
Inda Kungiyar agaji ta red Cross ta sanar da cewa adadin wadanda suka mutu yakai mutum 165 maimakon adadin 67 da suka fitar a baya saboda cigaba da neman wadanda abun ya shafa da Kungiyoyin agaji suka gudanar tun bayan faruwan lamarin.
Wani kanin sarkin gargajiya na Woro, Malam Ali Umar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa maharan sun mamaye al’ummar kauyen ne jim kadan bayan karfe 5 na yamma.
Ya ce maharan sun zo ne a kan babura inda suka kewaye al’umma kafin daga bisani su bude wuta kan mai uwa da wabi, don haka babu wanda zai iya tserewa.
Umar ya bayyana cewa an harbe mutanen da suka yi yunkurin guduwa, yayin da wadanda suka mika wuya aka tattara su a fadar hakimin kauyen, inda aka daure su aka harbe su.
Ya kuma bayyana cewa matar sarkin gargajiyar al’ummar garin Hauwa Umar da mahaifiyarsa da ‘ya’yansa uku na daga cikin wadanda aka sace yayin harin.
Ya kara da cewa "Hakan ya sa mutane biyar daga gidansa ba a san inda suke ba."
Umar ya ce al’ummar garin sun fada cikin firgici, inda jama’a da dama suka kauracewa gidajensu tare da barin garin kusan ba kowa.
"Abin da muke bukata a yanzu shine kara yawan jami'an tsaro don dawo da kwarin gwiwa da baiwa mutane damar komawa gidajensu," in ji shi.
Ya kara da cewa tun farko an samu rahotannin sirri na yiwuwar kai harin, wanda aka sanar da hukumomin kananan hukumomin tare da raba su ga manyan jami’an gwamnati.
Umar ya kara da cewa tun da farko wasu sojoji sun yi sintiri a yankin a ranar da aka kai harin, inda ya ce tun farko hakan ya dakile ‘yan ta’addan.
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda ya isa garin Kaiama a daren ranar Larabar da ta gabata tare da hakimai masu hidima da majalisar zartarwa, ya tabbatar da cewa an kashe musulman yankin su 75 saboda kin mika wuya ga masu tsattsauran ra'ayi da suke wa'azin wani bakon akida.
Gwamnan wanda ya jajanta wa al’ummar, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tura wata bataliya ta soji domin tabbatar da tsaro yankin.
Ya ce shirin tsaro an sanya masa suna Operation Savannah Shield.
"Daga baya an kai wadanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin, amma wasu an tura su Asibitin Koyarwa," in ji shi.
AbdulRazaq ya yi Allah-wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin harin matsorata.
Ya kuma jajantawa al’ummar Woro da Nuku, musamman iyalan wanda harin na ranar Talata ya shafa.
Tags
Labarai
_1.webp)