Bayan matsin lamba daga kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki, Majalisar Dattawa ta amince da kudirin gyaran dokar zabe amma ta yi watsi da bukatar sanar da sakamakon zaben ta hanyar na'ura, lamarin da wasu masu ruwa da tsaki ke ganin yana da matukar muhimmanci wajen gudanar da sahihin zabe a shekarar 2027.
Majalisar dattijai ta zartar da Dokar Zabe na 2022, Dokar gyara na shekaran 2026 bayan karatu na uku.
Ta kuma yi watsi da wani gyare-gyaren da aka yi a shafi na 60, karamin sashe na 3, na kudirin, wanda ke neman sanarwa da watsa sakamakon zabe ta hanyar na'ura.
Wannan matakin na nufin za'a cigaba sanar da Sakamakon zaben kamar yadda ake yi baya, Inda shugabannin Zabe a runfunar zabe zasu rinka mika sakamakon zabe ta hanyar cike takardun da aka tanadar daga kowace rumfar zabe zuwa wajen da aka tanadar domin tattara Sakamakon, bayan da Shugaban hukumar ya sanya hannu a kan fom din EC8A da tambari, sannan wakilan ‘yan takara suma sun sanya hannu.
_4.jpeg)