Wani magidanci ya kashe wani mutum a jihar Yobe Saboda zarginsa da yin lalata da matarsa.

Wani magidanci ya kashe wani mutum a jihar Yobe Saboda zarginsa da yin lalata da matarsa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da cafke wani mutum mai shekaru 50, Alhaji Hassan Umaru, bisa zarginsa da kashe, Sukari Abdul, mai shekaru 45, har lahira bisa zargin yin lalata da matarshi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa a ranar Lahadi, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Fabrairu, 2026, da misalin karfe 12:30 na rana. a kauyen Bundila dake karamar hukumar Gulani.

“A ranar 1 ga Fabrairu, 2026, da misalin karfe 12:30, hedkwatar ‘yan sanda ta Bara ta samu rahoton cewa wani Alhaji Hassan Umaru, mai shekaru 50, ya kashe wani mutum mai suna Sukari Abdul, mai shekaru 45, da ke kauyen Bundila, bisa zarginsa da yin lalata da matarsa,” in ji sanarwar.

Abdulkarim ya ce, arangama tsakaninsu ta yi kamari ne a cikin kasuwa, inda ake zargin wanda yayi kisan ya kai wa wanda aka kashen hari da adda.

“A cikin wannan arangama, wanda ake zargin ya sari wanda aka kashe da adda a dandalin kasuwa, inda nan take aka garzaya da wanda aka kashe zuwa cibiyar kula da lafiya a matakin farko na Bularaba domin kula da lafiyarsa, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa jim kadan bayan an kaishi.” Inji shi.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: