Falasdinawa 150 kawai Israi'la zata rinka bari shiga ƙasar Masar a kullum domin Neman magani ta mashigar Rafah.
Dubban Falasdinawa marasa lafiya da masu rauni suna ɗokin jira don tafiya kulawar gaggawa a ƙasashen waje yayin da Isra'ila ta sake buɗe kan iyakar Rafah da Masar don na dan wani Lokaci.
Mashigar ta Rafah wacce Isra'ila ta rufe ta kusan shekaru biyu - za ta yi aiki ne na tsawon sa'o'i shida a rana tare da barin mutane 150 kacal shiga ƙasar Masar domin Neman kulawar gaggawa game da lafiyarsu.
Hukumomin lafiya sun ce mutane 1,268 ne suka mutu a Gaza yayin da suke jiran samun magani lokacin da aka rufe Rafah, kuma likitocin sun yi gargadin cewa adadin zai karu matukar ba a bar wasu Falasdinawa suka fita cikin gaggawa ba.
Zuwa yanzu yakin kisan kare dangi da Isra'ila ta kaddamar a Gaza ya kashe akalla mutane 71,769 tare da raunata 171,483 tun daga watan Oktoban shekaran 2023.
Kimanin mutane 1,139 aka kashe a Isra'ila yayin harin da Hamas ta jagoranta a ranar 7 ga Oktoba, 2023, inda aka kama kusan 250 a Lokacin.
_8.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment