Harin da jirgin saman Rasha mara matuki yakai ya kashe ma'aikatan hakar ma'adinai 12 a Ukraine.

Harin da jirgin saman Rasha mara matuki yakai ya kashe ma'aikatan hakar ma'adinai 12 a Ukraine

Harin da jirgin saman Rasha mara matuki yakai ya kashe ma'aikatan hakar ma'adinai 12 a yankin Dnipropetrovsk na kasar Ukraine, tare da jikkata wasu mutum bakwai.

Akalla mutane 12 ne suka mutu Sakamakon wani hari da jirgin Rasha mara matuki ya kai kan wata motar safa da ke dauke da masu hakar ma'adinai a yankin Dnipropetrovsk da ke kudu maso gabashin Ukraine, kamar yadda ministan makamashin kasar ya sanar

"A yau, makiya sun kai wani hari mai ban tsoro da niyya kan ma'aikatan sashen makamashi a yankin Dnipro," in ji sanarwan na Ministan Makamashi Denys Shmyhal a shafinsa na Telegram ranar.

"Sakamakon harin ta'addancin, ma'aikatan hakar ma'adinai 12 ne suka mutu sannan wasu bakwai suka jikkata."

'Yan sanda sun ce an kai harin ne a birnin Ternivka. 
Hotunan da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar ta fitar ya nuna wata motar bas da ta kone tare da farfashewar tagoginta a gefen hanya.

Kamfanin makamashi na DTEK ya bayyana cewa, wadanda aka kashe da raunatawa, ma'aikatansa ne da suka dawo daga aiki.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: