Wanene Ayatollah Ali Khamenei? Jagoran da ya tsara ƙarfin tsayuwar Iran akan abokan gabanta.

Wanene Ayatollah Ali Khamenei? Jagoran da ya tsara ƙarfin tsayuwar Iran akan abokan gabanta.

Ayatollah Ali Khamenei, Shugaban Iran na Dindindin, wanda ya jagoranci ƙasar tun 1989 bayan rasuwar Ayatollah Ruhollah Khomeini, ya rasu ranar 28 Fabrairu 2026, Sakamakon harin da Israi'la da Amurka suka kai birnin Tehran. Khamenei, wanda aka haifa a Mashhad a shekarar 1939, ya yi karatu a Qom, ya zama shugaba mai ƙarfi wanda ya ɗaukaka tsarin tsaro da ikon sojojin ƙasar musamman rundunar juyin juya halin ƙasar, IRGC.

A lokacin mulkinsa, Khamenei ya dage kan ƙarfi da tsayuwar Iran, lokacin da ƙasar ke fuskantar barazana daga kasashen yamma, musamman Amurka da Isra’ila. 
Ya fadada ikon sojojin IRGC, inda suka zama jagorori a fannin tsaro da siyasa da tattalin arzikin Iran.

Khamenei ya fuskanci kalubale daga fitintinu na zanga-zanga a cikin ƙasar, ciki har da Zanga-zanga masu taken "Motsin Korewa" (2009) da zanga-zangar “Mata da Rayuwa da ’Yanci” a shekaran (2022), da kuma matsin tattalin arziki a farkon Wannan 2026. 
Gwamnatinsa ta mayar da martani da tsauraran matakai, wanda wasu suka ce ya ƙara ƙazantar da damuwar al’umma.

A fannin harkokin ƙasashen waje, Khamenei ya jagoranci Iran a matsayin jagora a abin da ya kira “turakan tsayuwa”, yana tallafawa abokan haɗin gwiwa a Lebanon da Syria da Iraq da Yemen da Palestine, yayin da ya ƙara ƙarfin shirin nukiliyan ƙasar.

Mutuwarsa ta zo ne a wani lokaci mai cike da tashin hankali, yayin da ƙasar ke fuskantar zanga-zanga da matsalolin tattalin arziki da rikici mai ƙarfi da Isra’ila da Amurka. Masana sun ce mutuwarsa na iya zama juyin juya hali a siyasar Iran, tana iya haifar da sauyi ko rikici tsakanin masu ra’ayin tsattsauran ra’ayi da masu son gyara tsarin mulkin ƙasar.

Ayatollah Ali Khamenei ya kasance mutum mai tasiri sosai a tarihin Iran na zamani, wanda ya kafa ƙasar da tsayayyar siyasa da tsaro, inda ya raba ra’ayoyi tsakanin magoya baya da masu suka.

News Translation in English Language.

Who Was Ayatollah Ali Khamenei? The Leader Who Shaped Iran’s Defiant Stance Against Its Adversaries.

Ayatollah Ali Khamenei, Iran’s Supreme Leader, who ruled the country from 1989 following the death of Ayatollah Ruhollah Khomeini, died on 28 February 2026 as a result of an attack carried out by Israel and the United States on Tehran. Born in Mashhad in 1939, Khamenei studied Islamic theology in Qom and rose to become a powerful leader who strengthened Iran’s security architecture, particularly the influence of the Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC).

Throughout his rule, Khamenei insisted on projecting strength and resistance, at a time when Iran faced what it viewed as persistent threats from Western countries, especially the United States and Israel. He expanded the authority of the IRGC, transforming it into a dominant force in Iran’s security, political, and economic spheres.

Khamenei’s leadership was repeatedly challenged by waves of domestic protests, including the “Green Movement” demonstrations of 2009 and the “Women, Life, Freedom” protests of 2022, as well as mounting economic pressure in early 2026. His government responded with harsh measures, which critics said deepened public discontent and social unrest.

In foreign policy, Khamenei positioned Iran as the central pillar of what he described as the “axis of resistance,” supporting allied groups and governments in Lebanon, Syria, Iraq, Yemen, and Palestine, while also intensifying Iran’s nuclear programme.

His death came at a time of heightened tension, with Iran grappling with internal protests, economic difficulties, and escalating confrontation with Israel and the United States. Analysts say his passing could mark a turning point in Iranian politics, potentially opening the door to reform or triggering power struggles between hardliners and advocates of political change.

Ayatollah Ali Khamenei remains one of the most influential figures in modern Iranian history, having shaped a state defined by political and security resilience, while deeply polarising opinion between supporters and critics.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form