Iran Ta Tabbatar da Rasuwar Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ƙasar, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei

Iran Ta Tabbatar da Rasuwar Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ƙasar, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei

Hukumomi a ƙasar Iran sun tabbatar da rasuwar Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ƙasar, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, sakamakon harin da Israel da Amurka suka kai birnin Tehran, a safiyar ranar Asabar.

Haka zalika kafofin watsa labaran gwamnatin Iran sun ruwaito cewa ‘yar Jagoran Ƙolin na Iran, Ali Khamenei, tare da surukinsa da jikanyarsa, suna cikin wadanda suka rasa ransu sakamakon hare-haren.

Biyo bayan wannan lamari, Majalisar Ministocin ƙasar ta sanar da ranakun makoki  na tsawon kwanaki 40, tare da hutu na kwanaki 7 a faɗin ƙasar, domin girmama marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da kuma bai wa al’umma damar halartar tarukan ta’aziyya.

Ana sa ran za a fitar da ƙarin bayanai kan yadda harin ya faru da kuma martanin ƙasashen duniya yayin da lamari ke ci gaba da bayyana.

News Translation in English Language.

Iran Confirms Death of Supreme Leader Ayatollah Sayyid Ali Khamenei

Iranian authorities have confirmed the death of the Supreme Leader of the Islamic Revolution, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, following military strikes carried out by Israel and the United States on the capital, Tehran, early on Saturday.

State-affiliated media in Iran reported that the Supreme Leader’s daughter, his son-in-law, and a grandchild were also among those killed in the attacks, which have sent shockwaves across the country.

In response to the incident, Iran’s Council of Ministers announced 40 days of national mourning, alongside a seven-day public holiday nationwide, to honor the late leader and allow citizens to participate in condolence ceremonies.

Authorities said further details on the circumstances surrounding the strikes and the reactions of the international community are expected to be released as developments continue to unfold.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form