Tinubu Ya Yi Raha Kan “Jar Hular” Gwamna Abba Kabir Yusuf A Taron Buda Baki A Abuja.

Tinubu Ya Yi Raha Kan “Jar Hular” Gwamna Abba Kabir Yusuf A Taron Buda Baki A Abuja.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi raha yayin da yake yi wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, barka da zuwa jam’iyyar APC, inda ya ce duk da haka gwamnan har yanzu na sanye da shahararriyar jar hula a kansa.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a jiya yayin wani taron buda baki na hadin gwiwa da aka shirya a Fadar Shugaban Ƙasa da gwamnoni a Abuja. 
Kalaman na sa sun haifar da dariya da nishadi a wajen taron, tare da jawo hankalin mahalarta.

Masu sharhi a fagen siyasa sun bayyana kalaman a matsayin raha ta siyasa, wadda ke nuni da alamar siyasar Kano da aka fi dangantawa da jar hula, lamarin da ya kara tayar da muhawara a kafafen sada zumunta.

News Translation in English Language.

Tinubu Jokes About Abba Kabir Yusuf’s “Red Cap” at Iftar Reception in Abuja.

President Bola Ahmed Tinubu made a light-hearted remark as he welcomed Abba Kabir Yusuf, Governor of Kano, to the All Progressives Congress (APC), joking that the governor was still wearing his trademark red cap.

President Tinubu made the comment during a joint iftar (breaking of fast) reception held at the Presidential Villa in Abuja. The joke drew laughter from guests and quickly sparked reactions among political observers.

Analysts described the remark as a playful political jab referencing Kano’s distinctive political symbolism, widely associated with the red cap, which has continued to generate debate on social media.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form