Kasashe kusan 20 tare da kungiyoyin kasa da kasa sun yi kakkausar suka kan matakan da Isra’ila ke dauka a Yammacin Kogin Jordan, suna bayyana su a matsayin “mamaya ta ainihi (de facto annexation)” wadda ke barazana ga makomar samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar a ranar 23 zuwa 24 ga Fabrairu 2026, ministocin harkokin waje daga kasashe daban-daban tare da kungiyoyi kamar Kungiyar Kasashen Larabawa da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi sun ce sabbin matakan Isra’ila na kara karfafa ikon ta a yankin da ake takaddama a kai, tare da raunana damar warware rikicin Falasdinu da Isra’ila ta hanyar mafitar kasashe biyu.
Sanarwar ta yi nuni da shirin Isra’ila na fara rajistar filaye a sassan Yammacin Kogin Jordan, musamman a yankin Area C, wanda zai iya janyo kwace filayen Falasdinawa da ke da matsalar takardun mallaka.
Masu suka sun ce hakan na bai wa Isra’ila damar mayar da filayen Falasdinawa “filayen gwamnati” da kuma hanzarta fadada matsugunnan Yahudawa.
Kasashen da suka rattaba hannu sun jaddada cewa matakan sun saba wa dokokin kasa da kasa da kuma shawarwarin Majalisar Dinkin Duniya, tare da ambaton ra’ayin shari’a na Kotun Duniya ta Kasa da Kasa da ya bayyana cewa ci gaba da mamayar Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan ba bisa doka ba ne.
Sanarwar ta kuma gargadi cewa ci gaba da aiwatar da wadannan tsare-tsare zai kara dagula zaman lafiya a yankin, ya kuma tauye ‘yancin Falasdinawa kan filayensu da rayuwarsu, tare da kawo cikas ga duk wani yunkuri na samar da dawwamammen zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Kasashen duniya da dama sun bukaci Isra’ila da ta dakatar da wadannan matakai, tare da komawa kan tattaunawar siyasa bisa dokokin kasa da kasa domin kare zaman lafiya da tsaro a yankin.
News Translation in English Language.
Nearly 20 Countries Condemn Israel’s ‘De Facto Annexation’ Drive in the West Bank.
Nearly 20 countries, alongside international and regional organisations, have strongly criticised recent measures taken by Israel in the West Bank, describing them as a “de facto annexation” that threatens the future of a viable Palestinian state.
In a joint statement issued between February 23 and 24, 2026, foreign ministers from several nations, together with bodies such as the Arab League and the Organisation of Islamic Cooperation, warned that Israel’s actions are entrenching its control over occupied Palestinian land and undermining prospects for a negotiated two-state solution.
The statement focused on Israel’s plan to begin land registration in parts of the West Bank, particularly in Area C, which is under full Israeli administrative and security control. Critics argue the process could enable the seizure of Palestinian land, especially from residents unable to provide formal ownership documents, and accelerate settlement expansion.
Signatories said the measures violate international law and contradict resolutions of the United Nations, as well as the advisory opinion of the International Court of Justice, which found Israel’s continued presence and settlement activity in the West Bank to be unlawful.
The countries warned that continuing these policies would further destabilise the region, dispossess Palestinians of their land, and deal a serious blow to efforts aimed at achieving lasting peace in the Middle East. They urged Israel to halt the measures and return to diplomatic negotiations grounded in international law.
Tags
Labarai
