Tinubu ya yabawa Shettima, inda ya ce abokin tafiya ne mai nagarta wajen ci gaban ƙasa.

Tinubu ya yabawa Shettima, inda ya ce abokin tafiya ne mai nagarta wajen ci gaban ƙasa.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Mataimakinsa, Kashim Shettima a matsayin “abokin tafiya mai matuƙar nagarta a fannin samun ci gaba.”

Shugaban ƙasar ya kuma sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kawar da ta’addanci da ’yan bindiga, yana mai cewa waɗannan munanan ayyuka ba su dace da al’adu da ƙimomin Najeriya ba.

Tinubu ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin yayin da yake buɗe Taron Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) a Cibiyar Taron Gidan Gwamnati da ke Abuja.

Yayin da yake gabatar da manyan baƙi, ya ambaci Shettima da cewa: “Mai Girma Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa, Kashim Shettima, abokin tafiya mai nagarta a fannin ci gaba,” lamarin da ya ja hankalin gwamnonin jihohi da ministoci da manyan jami’an gwamnati da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu da suka halarci taron.

A ci gaba da jawabin nasa, Shugaban ƙasar ya tabbatar wa ’yan Najeriya da ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa jami’an tsaro da dawo da zaman lafiya a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Ya kuma sanar da shirin ƙaddamar da yankuna bakwai na injinan noma (mechanisation zones) domin ƙara yawan amfanin gona da bunƙasa harkar noma.

Tinubu ya bayyana rashin tsaro a matsayin babban ƙalubalen tattalin arziki, yana mai jaddada buƙatar haɗin gwiwa tsakanin kowa da kowa domin shawo kan matsalar.

Da yake maraba da mahalarta taron na kwanaki biyu, Shugaban ƙasar ya ce taron na nuna aniyar bai ɗaya ta cimma ci gaban ƙasa.

Game da nasarorin gwamnatinsa, Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da ake aiwatarwa sun taimaka wajen daidaita tattalin arziki da dawo da amincewa a idon duniya.

Ya ƙara da cewa bunƙasa ababen more rayuwa a fannonin sufuri da wutar lantarki da haɗin intanet na zamani da gidaje da ban ruwa na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta bai wa muhimmanci.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi kira da a ƙara zurfafa haɗin gwiwa tsakanin matakan gwamnati uku, yana mai bayyana NEC a matsayin muhimmin dandali na tsara alkiblar tattalin arzikin Najeriya ta hanyar fahimtar juna. 
Ya kuma buƙaci mambobin majalisar da su bai wa rage talauci da samar da ayyukan yi da daidaita harkokin kuɗi muhimmanci.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form