Naira miliyan 36 kacal aka saki daga cikin Naira biliyan 218 na kasafin kuɗin kiwon lafiya na shekaran 2025, inji Minista lafiya.
Ministan Lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, ya bayyana cewa ma’aikatar ba ta samu damar aiwatar da kasafin kuɗin kiwon lafiyar ta na shekarar 2025 ba, sakamakon sakin Naira miliyan 36 kacal daga cikin Naira biliyan 218 da Majalisar Tarayya ta ware wa bangaren.
Farfesa Pate ya bayyana hakan ne yayin zaman kare kasafin kuɗin 2026 a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ayyukan Kiwon Lafiya.
Ya ce duk da cewa an saki gaba ɗaya kasafin kuɗin ma’aikata (personnel) na ma’aikatar kuma an kashe shi gaba ɗaya, ba haka lamarin yake ba ga ɓangaren kasafin kiwon lafiya, wanda ya ce ya fuskanci matsaloli musamman sakamakon tsarin bottom-up cash planning da Ofishin Babban Akanta na Tarayya ke aiwatarwa.
Ministan ya kuma shaida wa ‘yan majalisa cewa ma’aikatar ba ta samu damar amfani da wasu kuɗaɗen haɗin gwiwa ba, saboda jinkirin sakin gudunmuwar da Nijeriya ke bayarwa da lamarin da ya haddasa tsaiko wajen aiwatar da kasafin kudin 2025 sakamakon wasu yanayi da ba a zata ba.
Tags
Labarai
_1.jpeg)