Fira ministan Isra’ila zai gana da Shugaban Amurka, Donald Trump kan tattaunawar da Amurka ta yi da Kasar Iran.

Fira ministan Isra’ila zai gana da Shugaban Amurka, Donald Trump kan tattaunawar da Amurka ta yi da Kasar Iran.

Ofishin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sanar a da cewa zai gana da Shugaba Donald Trump a Washington ranar Laraba domin tattaunawa kan zaman tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran, yayin da Ministan Harkokin Waje na Iran ya yi barazana ga sansanin soja na Amurka a yankin matukar Amurka ta kai ma Iran hari, kwanaki ɗaya bayan tattaunawar a ƙasar Oman.

A cikin gajeren sanarwa, ofishin Netanyahu ya ce: “Firaminista na ganin duk tattaunawa dole ne ta haɗa da iyakance makamai masu linzami da kawo ƙarshen goyon bayan Iran ga ƙungiyoyin ta’addanci,” inda ya yi nuni da goyon bayan Iran ga ƙungiyoyi kamar Hezbollah a Lebanon da Hamas a Falasdinu. 
Netanyahu da Trump sun haɗu karon ƙarshe a watan Disamban 2025.

Amurka da Iran sun yi tattaunawa kai tsaye a Oman ranar Jumma’a, inda tattaunawar ta zama matakin farko kan yadda za a tattauna shirin nukiliyar ƙasar Iran, inda Trump ya bayyana tattaunawar a matsayin “mai kyau sosai” kuma ya ce za a ci gaba da a farkon mako mai zuwa. 

An wakilci Amurka ta hannun babban jakadan musamman kan Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, da Jared Kushner, surikin Shugaban ƙasar Amurka.

Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soja don tilasta Iran cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyar ta, bayan aika jirgin rundunar soja ta USS Abraham Lincoln da wasu jiragen yakin ruwa zuwa yankin, sakamakon ɗaukar mataki tsaurara da Iran ta yi a lokacin zanga-zangar ƙasa baki ɗaya wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

Haka zalika Suma Kasashen Larabawa na yankil Gulf na fargaban cewa hare-haren na iya haifar da yaƙi a yankin, musamman da tunanin yaƙin Israel-Iran na kwanaki 12 da ya faru a watan Yuni.

A ranar Asabar, Araghchi ya shaida wa Al Jazeera cewa idan Amurka ta kai hari kan Iran, ƙasar ba za ta iya kaiwa Amurka ba kai tsaye, “don haka dole ne ta kai hari ko mayar da martani ga sansanin sojan Amurka a yankin.”

Ya bayyana cewa akwai “rashin amincewa sosai” bayan abin da ya faru a tattaunawar da ta gabata, lokacin da Amurka ta kai hari akan cibiyoyin nukiliyar Iran a lokacin yaƙin Israi'la da Iran na bara.

Araghchi ya ce batun “makamai masu linzami” da sauran harkokin tsaro ba za a iya tattauna su ba, “ko yanzu ko a nan gaba.”

Tehran ta ce tattaunawar za ta kasance ne kawai kan shirin nukiliyar ƙasar. 
Sai dai Al Jazeera ta ruwaito cewa wakilan diflomasiyya daga Kasashen Masar da Turkiyya da Qatar sun gabatar da shawarwari ga Iran, wanda ke nufin za ta dakatar da samar da uranium mai tsanani na shekaru uku da fitar da uranium mai yawa daga ƙasar da kuma alkawarin “ba za ta fara amfani da makamai masu linzami ba.”

Sakataren Harkokin Waje na Amurka, Marco Rubio, ya sanar a ranar Laraba cewa tattaunawar dole ne ta haɗa da duk waɗannan batutuwa.

Isra’ila, babban abokiyar hulɗar Amurka, na ganin Iran na ƙoƙarin samar da makamin nukiliya kuma tana son a kawo ƙarshen shirin, duk da cewa Iran ta nace cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne. Isra’ila na son a dakatar da shirin makamai masu linzami na Iran da goyon bayan ƙungiyoyi masu tada kayar baya a yankin.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form