Ƙungiyar Transparency International, wata ƙungiya mai yaki da cin hanci da rashawa a duniya, ta sake bayyana Najeriya a matsayin ƙasa ta 142 mafi cin hanci a duniya a shekarar 2025.
Rahoton ya nuna cewa duk da wannan koma baya a matsayi, Najeriya ta ci gaba da kasancewa a matsayin ƙasa ta 142 mafi cin hanci a duniya kamar yadda ta kasance a shekarar 2024.
Ƙasashe kamar Cameroon, Guatemala da Guinea da Kyrgyzstan da Papua New Guinea sun yi daidai da Najeriya a matsayi ɗaya, duk suna da maki 26.
Rahoton da aka saki a shafin yanar gizon TI ranar Talata ya bayyana sakamakon Corruption Perceptions Index (CPI) na 2025.
A cikin wannan jerin, ƙasar Denmark ta ci gaba da zama ƙasa mafi tsafta da maki 89, sai ƙasar Finland da maki 88, sai Singapore da maki 84, sannan New Zealand da maki 81.
Babu wata ƙasa ta Afirka da ta shiga cikin ƙasashe 10 mafi tsafta, inda mafi yawansu ƙasashen Turai ne.
A nahiyar Afirka, ƙasar Seychelles da Cabo Verde da Botswana sun fi sauran ƙasashe tsafta, inda suke da maki 68, 62 da 58 bi da bi.
A gefe guda, Sudan ta kudu da Somalia da Venezuela sune ƙasashe mafi cin hanci a duniya a shekarar 2025.
Maíra Martini, Shugabar Transparency International, ta bayyana cewa rahoton CPI na 2025 yana ƙididdige ƙasashe 182 da yankuna bisa la’akari da yadda ake ganin cin hanci a fannin gwamnati. “Sakamakon ya dogara ne a sikeli daga 0 (matsanancin cin hanci) zuwa 100 (mai tsafta sosai),” in ji ta.
Martini ta ce: “Duk da cewa ƙasashe 31 sun rage matakan cin hanci tun daga 2012, yawancin sauran ƙasashe basu samu ci gaba ba, ko kuma matsalolin sun ƙara muni.” Ta kara da cewa, “Matsakaicin duniya ya kai sabon mataki mafi ƙasa na 42, kuma fiye da kaso biyu cikin uku na ƙasashe suna da maki ƙasa da 50.
Wannan na nufin mutane suna biyan farashin cin hanci, kamar rashin isassun asibitoci da ayyukan kariya daga ambaliyar ruwa da kuma raunana burin matasa.”
Ta yi gargadi cewa cin hanci babban barazana ne a kowane yanki na duniya, duk da cewa akwai alamun ƙaramin ci gaba. “Muna ganin raguwar jagoranci a yaki da cin hanci, har ma a ƙasashen demokradiyya irin su Amurka da Birtaniya da New Zealand.”
Martini ta jaddada cewa shugabanni dole su ɗauki mataki wajen yaki da cin hanci da sauran abubuwan da ke kawo raguwar gaskiya, kamar rage ikon doka da harin da ake kaiwa ga kungiyoyin farar hula masu zaman kansu.
Ta ce: “Zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da gwamnati a sassa da dama na duniya na nuna cewa mutane sun gaji da shugabanci mara lissafi kuma suna neman sauyi.”
Jerin Kasashen duniya da matakin cin hanci.
89 — Denmark — 1
88 — Finland — 2
84 — Singapore — 3
81 — New Zealand — 4
81 — Norway — 4
80 — Sweden — 6
80 — Switzerland — 6
78 — Luxembourg — 8
78 — Netherlands — 8
77 — Germany — 10
77 — Iceland — 10
76 — Australia — 12
76 — Estonia — 12
76 — Hong Kong — 12
76 — Ireland — 12
75 — Canada — 16
73 — Uruguay — 17
71 — Bhutan — 18
71 — Japan — 18
70 — United Kingdom — 20
69 — Austria — 21
69 — Belgium — 21
69 — United Arab Emirates — 21
68 — Barbados — 24
68 — Seychelles — 24
68 — Taiwan — 24
66 — France — 27
65 — Lithuania — 28
64 — Bahamas — 29
64 — United States of America — 29
63 — Brunei Darussalam — 31
63 — Chile — 31
63 — Saint Vincent and the Grenadines — 31
63 — South Korea — 31
62 — Cabo Verde — 35
62 — Israel — 35
60 — Dominica — 37
60 — Latvia — 37
59 — Czechia — 39
59 — Saint Lucia — 39
58 — Botswana — 41
58 — Qatar — 41
58 — Rwanda — 41
58 — Slovenia — 41
57 — Saudi Arabia — 45
56 — Costa Rica — 46
56 — Grenada — 46
56 — Portugal — 46
55 — Cyprus — 49
55 — Fiji — 49
55 — Spain — 49
53 — Italy — 52
53 — Poland — 52
52 — Malaysia — 54
52 — Oman — 54
50 — Bahrain — 56
50 — Georgia — 56
50 — Greece — 56
50 — Jordan — 56
49 — Malta — 60
48 — Mauritius — 61
48 — Slovakia — 61
47 — Croatia — 63
47 — Vanuatu — 63
46 — Armenia — 65
46 — Kuwait — 65
46 — Montenegro — 65
46 — Namibia — 65
46 — Senegal — 65
45 — Benin — 70
45 — Romania — 70
49 — Malta — 60
48 — Mauritius — 61
48 — Slovakia — 61
47 — Croatia — 63
47 — Vanuatu — 63
46 — Armenia — 65
46 — Kuwait — 65
46 — Montenegro — 65
46 — Namibia — 65
46 — Senegal — 65
45 — Benin — 70
45 — Romania — 70
45 — Sao Tome and Principe — 70
44 — Jamaica — 73
44 — Solomon Islands — 73
44 — Timor-Leste — 73
43 — China — 76
43 — Côte d’Ivoire — 76
43 — Ghana — 76
43 — Kosovo — 76
42 — Moldova — 80
41 — South Africa — 81
41 — Trinidad and Tobago — 81
41 — Vietnam — 81
40 — Bulgaria — 84
40 — Burkina Faso — 84
40 — Cuba — 84
40 — Guyana — 84
40 — Hungary — 84
40 — North Macedonia — 84
40 — Tanzania — 84
39 — Albania — 91
39 — India — 91
39 — Maldives — 91
39 — Morocco — 91
39 — Tunisia — 91
38 — Ethiopia — 96
38 — Kazakhstan — 96
38 — Suriname — 96
37 — Colombia — 99
37 — Dominican Republic — 99
37 — Gambia — 99
37 — Lesotho — 99
37 — Zambia — 99
36 — Argentina — 104
36 — Belize — 104
36 — Ukraine — 104
35 — Brazil — 107
35 — Sri Lanka — 107
34 — Algeria — 109
34 — Bosnia and Herzegovina — 109
34 — Indonesia — 109
34 — Laos — 109
34 — Malawi — 109
34 — Nepal — 109
34 — Sierra Leone — 109
33 — Ecuador — 116
33 — Panama — 116
33 — Serbia — 116
33 — Thailand — 116
32 — Angola — 120
32 — El Salvador — 120
32 — Philippines — 120
32 — Togo — 120
31 — Belarus — 124
31 — Djibouti — 124
31 — Mongolia — 124
31 — Niger — 124
31 — Turkey — 124
31 — Uzbekistan — 124
30 — Azerbaijan — 130
30 — Egypt — 130
30 — Kenya — 130
30 — Mauritania — 130
30 — Peru — 130
29 — Gabon — 135
28 — Bolivia — 136
28 — Iraq — 136
28 — Liberia — 136
28 — Mali — 136
28 — Pakistan — 136
27 — Mexico — 141
26 — Cameroon — 142
26 — Guatemala — 142
26 — Guinea — 142
26 — Kyrgyzstan — 142
26 — Nigeria — 142
26 — Papua New Guinea — 142
25 — Madagascar — 148
25 — Uganda — 148
24 — Bangladesh — 150
24 — Central African Republic — 150
24 — Paraguay — 150
23 — Congo — 153
23 — Eswatini — 153
23 — Iran — 153
23 — Lebanon — 153
22 — Chad — 157
22 — Honduras — 157
22 — Russia — 157
22 — Zimbabwe — 157
21 — Guinea-Bissau — 161
21 — Mozambique — 161
20 — Cambodia — 163
20 — Comoros — 163
20 — Democratic Republic of the Congo — 163
19 — Tajikistan — 166
17 — Burundi — 167
17 — Turkmenistan — 167
16 — Afghanistan — 169
16 — Haiti — 169
16 — Myanmar — 169
15 — Equatorial Guinea — 172
15 — North Korea — 172
15 — Syria — 172
14 — Nicaragua — 175
14 — Sudan — 175
13 — Eritrea — 177
13 — Libya — 177
13 — Yemen — 177
10 — Venezuela — 180
9 — Somalia — 181
9 — South Sudan — 181
Tags
Labarai
