Tinubu Ya Sauke Egbetokun, Daga Mukaminsa na Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya.

Tinubu Ya Sauke Egbetokun, Daga Mukaminsa na Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauke Kayode Egbetokun daga mukaminsa na Sufeton Janar na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (IGP), a wani mataki na bazata ga jama’a da masu sharhi kan harkokin tsaro.

Matakin ya biyo bayan wata ganawa ta musamman da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda aka umarci Egbetokun da ya mika ragamar mulki. Majiyoyi sun bayyana cewa matakin ya shafi sauye-sauyen shugabanci da gwamnati ke yi domin inganta tsaro da sake fasalin rundunar ‘yan sanda.

Rahotanni sun kuma nuna cewa Tunji Disu, wanda ke rike da mukamin Mataimakin Sufeton Janar na ‘Yan Sanda (AIG), an ayyana shi a matsayin wanda zai gaji Egbetokun, yayin da ake jiran sanarwa ta hukuma daga fadar shugaban ƙasa.

Kayode Egbetokun ya hau kujerar IGP ne a shekarar 2023, inda wa’adinsa ya kasance cikin cece-kuce musamman dangane da batun shekarun ritaya da gyaran doka da aka yi domin ci gaba da zamansa a ofis.

Masu sharhi sun ce sauyin shugabancin na iya zama wani sabon salo a kokarin gwamnati na magance matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar, yayin da jama’a ke jiran ganin irin matakan da sabon Sufeton Janar zai dauka.

Ana sa ran gwamnatin tarayya za ta fitar da cikakken bayani a hukumance nan ba da jimawa ba.

News Translation in English Language.

Tinubu Removes Egbetokun as Inspector-General of Police, Disu Set to Take Over.

President Bola Ahmed Tinubu has removed Kayode Egbetokun from his position as Inspector-General of Police (IGP), in a move that has drawn widespread attention across the country.

The decision followed a high-level meeting at the Presidential Villa in Abuja, where Egbetokun was directed to hand over the leadership of the Nigeria Police Force. Sources familiar with the development said the action is part of broader leadership changes aimed at strengthening internal security and reforming the police institution.

Reports indicate that Tunji Disu, currently an Assistant Inspector-General of Police (AIG), has been selected to succeed Egbetokun, pending an official announcement by the Presidency.

Egbetokun was appointed IGP in 2023, but his tenure was marked by controversy, particularly over issues surrounding retirement age and legal adjustments that allowed him to remain in office.

Security analysts say the leadership change could signal a new direction in the government’s efforts to address Nigeria’s security challenges, as citizens await policy priorities and reforms under the incoming police chief.

An official statement from the Federal Government confirming the appointment of the new Inspector-General of Police is expected shortly.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form