Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Biyan Kudin Fansa Ga Boko Haram kafin Sako daliban da aka sace a jihar Neja.


Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Biyan Kudin Fansa Ga Boko Haram kafin Sako daliban da aka sace a jihar Neja.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fito ta karyata rahotannin da ke ikirarin cewa an biya kudin fansa domin sakin daliban da aka sace a jihar Neja, tana mai cewa ba ta biya ko sisi ba ga ‘yan ta’addan.


A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta fitar, gwamnatin ta ce labaran da ke yawo na cewa an biya kudi ga Boko Haram ba su da tushe balle makama, kuma suna raina kokarin da jami’an tsaro suka yi wajen tabbatar da sakin wadanda aka sace.

Rahoton da AFP Suka fitar ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta biya makudan kudade na miliyoyin daloli domin tabbatar da sakin dalibai da ma’aikata 230 da aka sace daga Makarantar St. Mary’s Secondary da Primary School da ke Papiri a jihar Neja.

Rahoton ya ce an sace mutanen ne a wani harin da ‘yan bindiga suka kai makarantar, lamarin da ya tayar da hankula a fadin kasar, inda daga bisani aka samu nasarar sakin su bayan tattaunawa da kuma biyan kudin fansa.

Sai da gwamnatin ta jaddada cewa sakin daliban ya biyo bayan tsauraran dabarun tsaro da ayyukan leken asiri, ba tare da biyan kudin fansa ko sakin wani shugaban ‘yan ta’adda ba.

Haka kuma, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce dokokin kasa sun haramta biyan kudin fansa, domin hakan na kara karfafa ayyukan satar mutane da ta’addanci.

Duk da haka, wasu rahotannin kafafen waje sun yi ikirarin cewa an biya kudi a boye domin sakin daliban. Amma gwamnati ta nace kan matsayinta, tana mai cewa wadannan ikirari karya ne, kuma jami’an tsaro ne kadai suka kai ga nasarar sakin mutanen.

Gwamnatin ta bukaci ‘yan kasa da su yi watsi da jita-jita, tare da dogaro da bayanan hukuma daga mahukunta.

News Translation in English Language.

Federal Government Denies Paying Ransom to Boko Haram

The Federal Government of Nigeria has denied reports claiming that ransom was paid for the release of abducted students, stressing that no payment was made to any terrorists.

In a statement released by the Ministry of Information and National Orientation, the government described claims that funds were given to Boko Haram as “baseless and false,” emphasizing that such reports undermine the efforts of security agencies in securing the students’ release.

The statement confirmed that the students’ release was the result of coordinated intelligence operations and security measures, with no terrorist commanders released and no ransom paid.

The government also highlighted that Nigerian law prohibits ransom payments, as such payments can encourage further kidnappings and terrorism.

Although some foreign media reports have alleged that payments may have been made covertly to secure the students’ freedom, the government insists that these claims are untrue and that the success of the operation is solely due to the efforts of security forces.

Citizens have been urged to ignore rumors and rely on official updates from authorities.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form