A fannin kiwon lafiya, an samu gagarumin ci gaba bayan da aka haifi jariri na farko a Birtaniya ta hanyar dashen mahaifa daga mamaci.
An haifi jaririn, mai suna Hugo Powell, a asibitin Queen Charlotte da ke birnin Landan.
Mahaifiyar jaririn, Grace Bell, na fama da wata cuta ta haihuwa ne mai suna Mayer-Rokitansky-Küster-Hauser (MRKH) syndrome, wadda ke sa mace ta taso ba tare da mahaifa mai aiki ba.
A shekarar 2024, likitoci suka yi mata dashen mahaifa daga wata mace da ta rasu, a wani shiri na binciken likitanci da ke amfani da gabobin jiki daga mamata.
Bayan dashen, an yi amfani da fasahar IVF (In-Vitro Fertilization), inda ciki ya samu nasara har aka kai ga haihuwa lafiya.
Likitoci sun bayyana cewa wannan shi ne na farko a tarihin Birtaniya da aka samu haihuwa ta hanyar dashen mahaifa daga mamaci, sabanin na baya da aka yi daga masu rai.
Masana kiwon lafiya sun ce wannan nasara na nuni da sabon fata ga matan da ba su da mahaifa ko kuma wadanda mahaifarsu ba ta aiki, tare da bude sabon babi a maganin rashin haihuwa.
Iyalan jaririn sun nuna matukar godiya ga iyalan wadda ta bayar da mahaifar, suna kiran lamarin a matsayin “abin al’ajabi na rayuwa.”
A cewar likitoci, ana sa ran za a cire mahaifar da aka dasa bayan mahaifiyar ta kammala haihuwarta, domin kauce wa shan magungunan rage garkuwar jiki na dogon lokaci. Wannan nasara na kara jaddada rawar da kimiyya ke takawa wajen canza rayuwar bil’adama.
News Translation in English Language.
UK Records First Baby Born After Womb Transplant From Deceased Donor.
London, United Kingdom — A major medical milestone has been recorded in the United Kingdom following the birth of the country’s first baby delivered after a womb (uterus) transplant from a deceased donor.
The baby boy, named Hugo Powell, was born in December 2025 at Queen Charlotte’s and Chelsea Hospital in London. Medical experts described the development as a breakthrough in reproductive medicine.
The child’s mother, Grace Bell, was born with a rare congenital condition known as Mayer-Rokitansky-Küster-Hauser (MRKH) syndrome, which prevents the development of a functional womb. In 2024, she underwent a successful womb transplant using an organ donated by a deceased woman as part of a pioneering UK medical programme.
Following the transplant, doctors used in-vitro fertilisation (IVF) to achieve pregnancy, which later resulted in a safe delivery. Health professionals confirmed that this is the first successful birth in the UK involving a womb transplanted from a deceased donor, as earlier womb transplants in the country were carried out using living donors.
Medical specialists say the achievement offers new hope to women affected by uterine infertility and represents a significant step forward in fertility treatment. The family of the newborn expressed deep gratitude to the donor’s relatives, describing the birth as life-changing.
Doctors noted that the transplanted womb is usually removed once childbearing is complete, in order to avoid long-term use of immune-suppressing medication. The successful birth further highlights advances in transplant medicine and assisted reproduction in the UK.
Tags
Labarai
