Dakarun sojin Najeriya sun kama wani da ake zargin dillalin makamai ne tare da kwace manyan bindigogi da harsasai 969 a wani gagarumin samamen tsaro da suka gudanar a jihar Taraba.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Brigade ta 6 ta Rundunar Sojin Kasa, Sashen 3 na "Operation Whirl Stroke", sun kama wanda ake zargi ne a lokacin da suke gudanar da aikin binciken ababen hawa a Sarkin Kudu a ƙaramar hukumar Ibi.
An ce wanda aka kama mai suna Monday Reuben, dan shekara 48, dan asalin Numan a Jihar Adamawa ne.
Abubuwan da aka kwace sun hada da:
Bindigogi AK-47 guda biyu
Majallun harsasai 197 (fanko)
Harsasai 250 na 7.62×51mm NATO
Harsasai 700 na 9mm
Harsasai 19 na 7.62mm (na musamman)
Kudi ₦2,440,000
Wayoyi da katunan ATM da takardun shaida
Layu da wasu kwalaben turare
Rundunar sojin ta ce an gudanar da aikin ne bisa sahihan bayanan sirri, inda sojojin suka dakatar da motar wanda ake zargin suka kuma gano makaman bayan bincike.
A cewar sanarwar rundunar, wanda ake zargin da dukkan kayayyakin da aka kwace suna hannun hukuma, kuma za a mika su ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da daukar matakan shari’a.
Sojojin sun jaddada kudirinsu na ci gaba da yaki da safarar makamai da duk wani nau’in ta’addanci domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar Taraba da ma yankin Arewa maso Gabas baki daya.
Tags
Labarai
